Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministan Rasha Yaje Yankin Kirimiya

Firayim minista Dmitry Medvedev (hagu) da shugaba Vladimir Putin (dama). Danjuma da Danjummai?
Firayim minista Dmitry Medvedev (hagu) da shugaba Vladimir Putin (dama). Danjuma da Danjummai?

Firayim Ministan Rasha Dmitry Medvedev na yankin Crimea. Shi ne mafi babban mukami cikin jami'an Rasha da su ka je Crimea tun bayan da Rashar ta karbe yankin daga Ukraine a farkon wannan watan.

Firayim Ministan Rasha Dmitry Medvedev na yankin Crimea. Shi ne mafi babban mukami cikin jami'an Rasha da su ka je Crimea tun bayan da Rashar ta karbe yankin daga Ukraine a farkon wannan watan.

Mr. Medvedev ya ce ya na jagoranci ne ga wata tawagar jami'an Rasha don wani taron kan abin da ya kira "ciyar da tsibirin gaba."

Firayim Ministan ya ce Rasha za ta kirkiro wani yanki na habbaka tattalin arziki a Crimea, inda za a rika karfafa gwiwa ma masana'antu, ta wajen rage masu haraji da kuma gindaya masu ka'idoji masu sauki. Mr. Medvedev ya kuma ce za a kyautata albashi da fensho a yankin na Crimea.

Taron da ya jagoranta yau, ya zo ne kwana guda bayan da Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry, ya bukaci Rasha ta janye dubban sojojinta da ke girke daura da kan iyakokin Ukraine a gabas da yamma.

Keryy ya gaya ma Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov a birnin Paris jiya Lahadi cewa sojojin na haddasa yanayi na fargaba a kasar Ukraine kuma kasancewarsu a wurin bai taimakawa a diflomasiyyance.

Lavrov bai yi magana kai tsaye game da sojojin Rasha ba. To amma a tsawon makon jiya, ya yi ta kokarin tabbatar ma Amurka cewa Rasha ba ta da wani shiri na ketara kan iyakar Ukraine.

Kerry ya ce da shi da Lavrov sun amince cewa 'yan kasar Ukraine na da 'yancin zabar makomarsu.
XS
SM
MD
LG