Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Mnistan Pakistan Yousuf Raza Gilani na gwagwarmayar ganin jam’iyyarsa ta cigaba da rike ragamar iko


Shugabannin siyasa a kasar Pakistan

Firayim Mnistan Pakistan Yousuf Raza Gilani na gwagwarmayar ganin jam’iyyarsa ta cigaba da rike ragamar iko

Firayim Mnistan Pakistan Yousuf Raza Gilani na gwagwarmayar ganin jam’iyyarsa ta cigaba da rike ragamar iko a yau dinnan Litinin, bayan da abokiyar tafiyar jam’iyyarsa a gamayyarsu ta yi shelar canza sheka zuwa banagren ‘yan adawa.Yana ganawa da shugabannin ‘yan adawa kwana guda bayanda matokarar tsayuwar siyasar kasar ta tasar ma kocewa, saboda Jam’iyyar Muttahida Qaumi, ko MQM a takaice, ta ce za ta koma bangaren adawa a Majalisar Wakilai da ta Dattawa.Jam’iyyar MQM ta shiga takaddama da gwamnati game da batun garanbawul a bangaren haraji, karin farashin man fetur da kuma yinkurin inganta matakan tsaro.Ya zuwa yanzu dai babu haske game da ko ficewar MQM daga gamayyar da ke shugabanci za ta kayar da gwamnatin Firayim Minista Gilani, wadda kafin nan ke da dan rinjaye a Majalisa.

XS
SM
MD
LG