Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fiye Da Mutane 48 Ne Aka Kashe A Gaza A Cigaba Da Fada Da Ake Yi A Yankin...


Hayaki yake tashi daga Gaza, bayan wani farmaki da Isra'ila ta kai a can ranar Asabar.
Jami’ai a yankin Falasdinu sun ce an kashe fiye da mutane 48 a zirin Gaza, tun lokacinda Isra’ila ta kaddamar da hare hare a yankin ranar laraba data shige.
Wani mutm yake bi ta cikin baraguzan ofishin Frayin ministan Hamas Ism'ail Haniyeh, bayan hari da isra'ila ta kai kan ofishin.
Wani mutm yake bi ta cikin baraguzan ofishin Frayin ministan Hamas Ism'ail Haniyeh, bayan hari da isra'ila ta kai kan ofishin.

‘Yan jarida uku dake aiki da kafofin yada larabai na larabawa sun jikkata, lokacin da wani farmaki daga sama da Isra’ila ta kai, ya fadi kan ofishin kafar yada laraban larabawa a yau lahadi.

Isra’ila tana ci gaba da fatattakar yankin a yau lahadi ma, ta wajen auna wasu hare haren ta sama da kuma ruwa, kan wasu cibiyoyi, martani kan cigaba da kai mata hare hare da rokoki.

Jiya Asabar, shugaban Masar Mohammed Morsi, ya karbi bakuncin shugabnnin Hamas, da na wasu kwayenta biyu, Qatar da turkiyya domin shawarwari kan hanyoyi da za a bi na kawo karshen fadan. Kamar yadda ya fada da kalamansa, shugaban na Masar yace “akwai wasu alamun za a cimma tsagaita wuta nan bada jumawa ba, amma bamu sami tabbacin hakan ba tukun".

A gefe daya kuma, ministocinn harkokin wajen kungiyar hada kan kasashen larabawa mai cibiya a Alkahira, sun yi wani zaman gaggawa domin tattaunawa kan martanin kasashensu kan wannan fada.
XS
SM
MD
LG