Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan wasan Flamingos Sun Sauka A Abuja Bayan Lashe Tagulla A Gasar Cin Kofin Duniya Ta Mata


'Yan wasan Flamingos na Najeriya a lokacin da suke murnar lashe kyautar tagulla a gasar cin duniya ta mata 'yan kasa da shekara 17 a India (Facebook/NFF)
'Yan wasan Flamingos na Najeriya a lokacin da suke murnar lashe kyautar tagulla a gasar cin duniya ta mata 'yan kasa da shekara 17 a India (Facebook/NFF)

Najeriya ta doke Jamus a bugun fenariti bayan da aka tashi 3-3 a wasan neman gurbi na uku a gasar.

‘Yan wasan Flamingos sun sauka a Abuja, babban birnin Najeriya bayan da suka lashe kyautar tagulla a gasar cin kofin duniya ta mata ‘yan kasa da shekara 17 da aka yi a India.

Najeriya ta doke Jamus a bugun fenariti bayan da aka tashi 3-3 a wasan neman gurbi na uku a gasar.

Tawagar ‘yan wasan ta sauka a filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe a ranar Talata inda jami’an hukumar kwallon kafar Najeriya ta NFF suka tarbe su.

Jim kadan bayan saukarsu, ministan wasanni da matasa, Sunday Dare, ya gana da ‘yan wasan inda ya ba su tabbacin cewa gwamnati za ta taimaka musu ta yadda za a karfafa tawagar.

Rahotanni sun yi nuni da cewa Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa, ya bai wa tawagar ‘yan wasan kyautar miliyan uku kuma nan take da suka sauka aka ba su cek din kudin.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG