Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gabashin Kudus Ne Babban Birnin Falasdinu - Inji Erdogan


Shugaban Kasar TurkiyyaTayyip Erdogan Da Takwaransa Mahmoud Abbas Na Falasdinu A Wajen Taron.
Shugaban Kasar TurkiyyaTayyip Erdogan Da Takwaransa Mahmoud Abbas Na Falasdinu A Wajen Taron.

Kungiyar kasashen musulunci sun yi wani zama akan hukuncin da shugaban Amurka Donald Trump ya yakce, na cewar birnin Kudus shine sabon babban birnin Isra'ila.

Shugabanni 22 daga kasashen Musulmin sun taru a birnin Istanbul a yau Laraba don mayar da murtani akan matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka akan amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila.

Wannan taron na zuwa ne yayin da ake ci gaba da dauki ba dadi a gabas ta tsakiya, gami da sukar da ake ci gaba da samu game da matakin na birnin Kudus.

Ana yin wannan ne karkashin inuwar kungiyar kasashen Musulmi mai wakilai 57 da ake kira OIC a takaice. Kasar Turkiyya ce ke shugabantar kungiyar a yanzu haka, kuma Shugaba Racep Tayyip Erdogon ne ya kira taron na gaggawa.

Erdogan ya fadawa shugabannin da suka taru a farkon taron yau Laraba cewa, “ina kira ga kasashen da suke mutunta dokokin kasa da kasa, da kamanta gaskiya, su amince birnin gabashin Kudus da aka mamaye shine babban birnin Palasdinawa.”

Shugabannin Mahmud Abbas na Falasdinu da Sarki Abdallah na Jordan da IIham Aliyev na kasar Azerbaijan da Abdoul Hamid na Bangladesh da kuma Hassan Rouhani na Iran, suna cikin mahalarta wannan taron.

Masar da Saudi Arabiya, tare da wasu kasashe 23, za su halarci taron amma a matakin ministocin harkokin kasashen waje.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG