Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ganduje Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC


Sabon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje (Facebook/Gandujiyya Online)
Sabon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje (Facebook/Gandujiyya Online)

A tsakiyar watan Yulin da ya gabata tsohon shugaban jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus daga mukaminsa.

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta zabi tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin sabon shugabanta.

APC ta zabi Ganduje ne a babban taronta da ke gudanar a Abuja.

Kazalika jam’iyyar ta zabi Ajibola Bashir a matsayin sabon babban sakatarenta.

A tsakiyar watan Yulin da ya gabata tsohon shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu ya yi murabus daga mukaminsa wanda aka zaba a watan Maris din 2022.

Bashir ya maye gurbin Sanata Iyiola Omisore wanda shi ma ya ajiye aikinsa rana daya da Adamu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG