Accessibility links

Gara In Kashe Kaina Da A Tasa Keyata Zuwa Amurka- Kashamu

  • Grace Alheri Abdu

Zababben dan majalisar dattijai daga jihar Ogun Buruji Kashamu yace gara ya kashe kansa da ya bari a tasa keyarsa zuwa Amurka domin amsa laifin safarar hodar Ibilis.

Wata kotun tarayya a Lagos tace hukumar NDLEA mai yaki da safara da kuma shan muggan kwayoyi tana da hurumin kama zababben dan majalisar dattijai daga jihar Ogun Buruji Kashamu, tare da furfanar da shi a gaban kuliya.

Sai dai alkalin kotun Ibrahim Buba yace hukumar tayi riga malam masallaciu da ta yiwa gidan dan majalisar kawanya kafin samun izinin kotu.

A cikin hirarsu da wakilinmu Babangida Jibril, shugaban hukumar Ahmed Giade ya bayyana cewa, sun killace gidan ne,sabili da akwai bukatar da gwamatin Amurka ta gabatar ga gwamatin Najeriya tana bukatar a mika shi ga gwamnatin Amurka, bisa tuhumarshi da Amurka ke yi da safarar hodar ibilis, da ya yi zuwa Amurka.

Shugaban hukumar NDLEA ya bayyana cewa, basu sami kama Mr. Kashamu ba sabili da ya kulle kansa a bandaki, ya kuma ce gara ya kashe kansa da a kama shi a tasa keyarsa zuwa Amurka.

Ga cikakken rahoton.

XS
SM
MD
LG