Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana, Afirka Ta Kudu Sun Kafa Asusun Bunkasa Nahiyar Afrika


Ghana Da Afirka Ta Kudu Sanar Da Bude Asusun Ci Gaban Nahiyar Afirka
Ghana Da Afirka Ta Kudu Sanar Da Bude Asusun Ci Gaban Nahiyar Afirka

Kasar Ghana tare da Afrika ta kudu sun sanar da bude wani asusun ci gaban nahiyar Afrika wato 'Africa Prosperity Fund,' asusun da ake sa ran zai taimaka wajen ci gaban kasashen nahiyar a fannin gine-gine da tattalin arziki da neman ilimi da ci gaban matasa da mata da dai sauransu.

KUMASI, GHANA - Shugaban Ghana Nana Addo ya sanar da bude kan wannan asusun yayinda ake shan biki ranar al’umma ta duniya wato Global Citizen Festival a Ghana.

Shugaban na Ghana ya bayyana cewa "wannan asusun da zai tattara biliyan daya na dalan Amurka domin al’ummar Afrika ya taimaka wajen samar da ci gaban Nahiyar ta fanni daban-daban ciki harda bunkasa harkar gine-gine da tattalin arziki da neman ilimi da baiwa mata da matasa damar makinda suke bukata, da bunkasa harkar kiwon lafiya da fasahar zamani”

“Wannan assusn zai kasance karkashin yarjejeniyar kasuwanci mara shige tsakanin kasashen Nahiyar Afrika. Matakinda shugaba Nana Addo ya bayyana cewa zai bada gudunmawa wajen shawo kan matsalar raunin tattalin arziki da kasashen Nahiyar ke fama dashi.

Masanin tattalin arzikin kasa da kasa kuma lakcara a Jami'ar Christ The King University College a Ghana ya ce wannan asusu kasancewa ba na kasa daya ba ce, na Afrika baki daya ne, zai taimaka sosai amma sai an samu masu sanya idanu akan adana kudaden tare da lissafi, hakan zai taimaka.

To sai dai ta fanni kare hakkokin mata da matasa Malama Fauziyya Adam mai fafutukan kare hakkokin mata a Ghana ta yi marhaba da wannan asusun. Ta ce zai yi taimako sosai sabode mata an bar su baya amma kuwa ba su bar kan su baya ba. Duk inda za'a isa ana yi ma mana kallon raunannu ne adon haka sai ana barin su a baya. Ta ce “muna farin ciki da samun labarin wannan asusun da zai maida hankali wajen karfafa mata"

Sai dai kafin wannan taron an bukaci shugabannnin duniya da suka kammala taro a majalisan dinkin duniya karo na sabain da bakwai a birnin New York da manya manyan masana'antu tare da kungiyoyin bada lamuni da su bada gudunmuwa wajen shawo kan matsalar matsanancin talauci a duniya.

Saurari cikakken rahoto daga Hamza Adam:

Ghana, Afirka Ta Kudu Sun Kafa Asusun Bunkasa Nahiyar Afrika.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

XS
SM
MD
LG