Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana, Uruguay Sun Fice A Gasar Cin Kofin Duniya


'Yan wasan Ghana, Uruguay suna jimamin ficewa daga gasar cin kofin duniya AP
'Yan wasan Ghana, Uruguay suna jimamin ficewa daga gasar cin kofin duniya AP

Ita dai Koriya ta Kudu ta shammaci Portugal ne ta zura mata wata makararriyar kwallo, wacce ita ta tilastawa Uruguay ficewa.

Uruguay da Ghana sun yi sallama da gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar, duk da nasarar da Uruguay din ta samu a wasan da suka kara a ranar Juma’a.

Uruguay ta lallasa Ghana da ci 2-0, amma doke Portugal da Koriya ta Kudu ta yi a rukunin H da ci 2-1, ya sa Uruguay ta gaza tsallakawa zagaye na gaba.

Dan wasa Luiz Suarez ya taka muhimmiyar rawa a kwallayen da Uruguay ta ci ta hannun Giorgian De Arrsacaeta.

Ita dai Koriya ta Kudu ta shammaci Portugal ne ta zura mata wata makararriyar kwallo, wacce ita ta tilastawa Uruguay ficewa.

An dai cire Suarez a wasan kafin a kammala, inda aka nuna shi yana rufe fuskarsa bayan da aka tashi a wasan.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG