Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gidajen Sinima Sun Amince Zasu Nuna Fim Din Daya Jawo Ce-Ce-Ku-Ce


Gidan Sinima
Gidan Sinima

Masu sha’awar kallon fina-finai yau sun bazama da yawansu zuwa gidajen sinima domin kallon wannan fim din daya jawo ce-ce ku-ce, bayan sauyin shawara da kamfanin Sony yayi na haska wannan fim.

Gidajen sinima masu zaman kansu sunce zasu nuna fim din mai suna The Interview, biyo bayan yanke shawara da manyan gidajen sinima suka yi, na cewa baza su haska fim din ba saboda barazana.

Kamfanin na Sony ya kuma saki wannan fim akan shafukan Youtube, Google Play da na’urar wasa da ake kira Xbox.

Evan Goldberg da Seth Rogen mutane biyu da suka bada umarnin hada fim din sun hallarci haska shi jiya da tsakar dare a birnin Los Angeles, har suke ta godewa magoya bayansu. Da yawa daga cikin wadanda suka kalli wannan fim sun bayyana cewa babu wanda yake da ikon gaya musu abunda zasu iya gani da abunda baza su iya gani ba. Suma manajojin gidajen siniman sunce suna goyon bayan ‘yanci ne dangane da wannan batu.

Wannan fim mai suna The Interview dai labari ne na ‘yan jarida guda biyu da ma’aikatar tattara bayanan sirrin Amurka ta dauka domin kashe shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un.

Koriya ta Arewa tayi Allah wadai da wannan fim, tana mai cewa ya keta diyaucinta.

A farkon wannan watan ne wasu da ba’a san ko su waye ba, suka saci shiga cikin komfutocin kamfanin Sony inda suka sace bayanai masu matukar muhimmanci.

Amurka na zargin Koriya ta Arewa da kawo harin, ita kuma Koriyar ta ce sam-sam babu ruwanta.

XS
SM
MD
LG