Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Girgizar Kasa Ta Afkawa Tsakiyar Kasar Italiya


Mau aikin ceto na zakulo wani yaro da ya makale a baraguzan gini
Mau aikin ceto na zakulo wani yaro da ya makale a baraguzan gini

A Italiya, girgizar kasa mai karfin gaske ta afkawa tsakiyar kasar, ta haddasa barna mai yawa ga yankuna da suke kusa da inda ta faro, har ta halaka mutane 37.

Hukumar kula da lamura a karkashin kasa ta Amurka ta kiyasta karfin girgizar ya kai maki shida da digo biyu a sikelin, girgizar ta auku ne a wani wuri mai tazarar kilomita 10 gudu maso gabashin garin da ake kira Norcia. Anji motsin kasa a wurare msu nesa daga inda girgizar ta samo asali, har a babban birnin kasar Rome, mai tazarar kilomita 150 daga Norcia.

Ana zakulo mutane
Ana zakulo mutane

Girgizar ta auku ne da misalin karfe 3:30 na safe, sannan aka samu karin wasu kanana daga bisani. Wata hukumar tsaron kasar ta farin kaya tace daruruwan mutane sun jikkata, wasu masu yawa suna bukatar muhalli na wucin gadi.

"Girgizar kasa mai karfin gaske haka, kuma a inda ta auku galibi zata rusa gine gine, wanda zai janyo mace-mace," inji shugaban hukumar mai suna Fabrizio Curcio.

XS
SM
MD
LG