Accessibility links

Girgizar Kasa Ta Jijjiga Gabashin Kasar Turkiyya


Ma'aikatan ceto na kokarin kubutar da mutanen da suka makale a karkashin buraguzai a kauyen Tabanli, bayan girgizar kasar da aka yi a gabashin kasar Turkiyya ranar Lahadi 23 ga watan Oktoba

Talbijin ya nuna bidiyon ruguzazzun gine-gine da kuma motoci a mammalkwade

An yi wata kakkarfar girgizar kasa a kudu maso gabashin kasar Turkiyya a kusa da kan iyakar tad a kasar Iran.

Hukumar nazarin fasalin karkashin kasa ta Amurka ta ce girgizar kasar mai karfin awo 7 da digo 3 da kuma zurfin kilomita 7 da digo 2 ta wakana ne da yammacin yau Lahadi a lardin Van.

Kamfanin dillancin labaran Anatolian na gwamnatin kasar Turkiyya ya ce dimbin gine-gine sun rushe kuma an yi fama da kananan jijjigar kasa bayan kakkarfar girgizar, kuma ya ce mutum hamsin a kalla sun ji ciwo.

Bayanan cibiyar saka idanu da binciken girgizar kasa ta Kandili a kasar Turkiyya, sun nuna cewa awo 6 da digo 6 ne karfin girgizar kasar kuma zurfin ta kilomita 5.

Mataimakin Frayim Ministan kasar Besir Atalay ya ce gine-gine 25 zuwa 30 sun rushe, wani ginin kwana ya rushe a garin Ercis, kuma wasu gine-gine 10 sun rushe a birnin Van.

Talbijin ya nuna bidiyon ruguzazzun gine-gine da kuma motoci a mammalkwade, kuma an ga dimbin mutane rike da shebur da manjagara su na tonon burguzai su na neman mutanen da ke da sauran rai.

Mutane na ceton wata matar da ta makale a karkashin buraguzai bayan kakkarfar girgizar kasar da ta yi awo 7 da digo 2 wadda ta ruguza gine-gine kimanin 45 a gabashin kasar Turkiyya
Mutane na ceton wata matar da ta makale a karkashin buraguzai bayan kakkarfar girgizar kasar da ta yi awo 7 da digo 2 wadda ta ruguza gine-gine kimanin 45 a gabashin kasar Turkiyya

Magajin garin Ercis ya gabatar da kiran neman taimakon gaggawa, kuma ya ce dimbin mutane sun mutu.

XS
SM
MD
LG