Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabbin Gobara A Kasuwannin Ngurore Da Numan A Jihar Adamawa.


gobara tana ci

Wadannan bala'o'in suna zuwa ne kasa da kwanaki biyu bayan tashin wata gobarar a babbar kasuwar Jimeta-Yola, fadar jihar Adamawa.

Yayin da ake alhinin gobarar data lakume rabin kasuwar Yola, yanzu kuma wata sabuwa ta auku,indawata gobarar ta sake tashi a kasuwannin garin Numan da kuma Ngurore, inda aka yi hasarar dukiya na miliyoyin naira.

Wannan tashe tashen gobarar da ke aukuwa a jihar yanzu ya jefa yan kasuwa cikin fargaba da rashin sanin tabbatas.

Saboda haka ne ma gwamnatin jihar ta kafa kwamitin bincike karkashin mataimakin gwamnan jihar wanda zai duba musabbabin tashe tashen gobarar, da kuma irin matakai da suka kamata a dauka domin hana haka sake aukuwa.

Gwamnan jihar Adamawa Senata Muhmmadu JIbrilla ne ya bayyana haka lokacinda yake jaje ga 'yan kasuwa da al'umar da jihar wadanda wannan bala'i ya shafa.

Ga karin bayani.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG