Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Kashe Mutane 23 A Malaysia


 Jami'an Yan Sanda A Kuala Lumpur, Malaysia Tare Da Ma'aikatan Kashe Gobara Na Shirin Fito Da Gawarwakin Wadanda Suka Kone.
Jami'an Yan Sanda A Kuala Lumpur, Malaysia Tare Da Ma'aikatan Kashe Gobara Na Shirin Fito Da Gawarwakin Wadanda Suka Kone.

Ya zuwa yanzu jami'ai na binciken dalilin da ya haifar da gobarar, duk da dai jami'ai na kyautata zaton wutar lantarki ce ta haifar da ita.

Wata gobara da ta tashi da sassafe a wata makarantar addini mai zaman kanta a babban birnin Malaysia, Kuala Lumpur tayi sanadiyyar mutuwar mutane 23 a yau Alhamis, aka sarin su matasa maza.

Jami’an kashe gobara sun ce gobarar ta asuba a Darul Qur’an Ittifaqiyya ta fara ne a dakin kwanan dalibai a saman bene inda daliban ke bacci. Wadanda suka mutun sun hada da yara maza yan tsakanin shekaru 13 zuwa 17, da kuma Manya Malamai guda biyu, sun kasa fita ne sakamakon hanyar fita daga dakin guda daya wuta ta mamaye ta kuma tagogin dakin duk an rufe su da karafa.

Hakanan wadanda suka ganewa idanuwansu suka tsaya babu yadda zasu yi suna jin ihun yaran yayin da wutar take ci. An sami gawarwakin su a dunkule wuri guda a kwana bayan dakin ya kone.

Jami’an kashe gobara sun ce akwai yiwuwar daliban sun mutune sakamakon Hayaki da suka shaka.

An ceci dalibai goma sha takwas daga gidan, shida daga cikin su an kaisu asibiti cikin mummunan hali.

Ya zuwa yanzu ana gabatar da bincike akan abinda ya haddasa wutar, amma jami’ai suna zaton lantarki ce ta jawo.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG