Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta kashe Mutane Akalla 43 A Indiya


Akalla mutane 43 ne suka mutu, sanadiyyar wata gobara da ta tashi a wani kamfani a New Delhi, babban birnin kasar India a jiya Lahadi.

Jami’ai sun ce wutar ta tashi ne da safe a ginin mai hawa 6 inda leburori su ke bacci, a tsohon garin birnin da ke kusa da yankin kasuwa mai cike da hada-hadar jama’a.

Masu ceto sun kai wadanda lamarin ya rutsa da su a asibiti. An yi wa wasu mutane 16 maganin kunar wuta ko kuma shakar hayaki suka kuma wartsake.

Jami’ai sun ce ana binciken musabbabin tashin gobarar da ta soma da misalin karfe 5:30 na safe.

Motocin kashe gobara 25 suka yi aikin kashe wutar, kuma tuni aka kammala aikin ceto, a cewar jami’in ‘yan kwana-kwana, Atul Kumar Gargs.

“Mun fitar da kusan mutane 52, an sanar da mu ne da karfe 5 da minti 22 na safe, kuma da farko mun tura motoci 4, ya zuwa yanzu motocin kashe gobara 35 muka tura, tare da adadin jami’ai 150.

An kai mutanen da aka ceto a asibitoci daban-daban. Ana iya samun adadin wadanda suka mutu da wadanda suka tsira a asibitocin. Kimanin mutane 2 kuma suna cikin karikicen har yanzu”.

Firai Minista Narenda Modi, ya bayyana gobarar a matsayin “babban ibtila’i”.

Tashin gobara ya kasance ruwan dare a Indiya, inda masu gini da mazauna ke take dokokin gine-gine.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG