Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Lakume Daruruwan Shaguna A Jihar Sokoto


Da misalign karfe 10pm na daren lahadi ne gobara ta tashi a babbar kasuwar Dan Jabalu cikin jihar Sokoto, kuma ta dauki sa’o’i tana ci, lamarin da yayi sanadiyyar konewar daruruwan shaguna da akasarin su shagunan tufafi ne, da zinare, da azurfa da kuma shagunan canjin kudaden waje.

Kasuwar wacce ake yiwa lakabi da kasuwar Dan Jabalu, dake tsohuwar kasuwar Sokoto makekiyar kasuwa ce mai shagunan sama hawa guda wadanda suka yi da’ira tare kuma da wasu shagunan a tsakiya.

Duk da cewa hukumar kashe gobara sun kai dauki, amma hakan bai hana wutar zagaye daukacin shagunan ba, lamarin da yasa wasu masu shaguna suka yi zargin sakacin hukumar da munanar lamarin.

Malam Abdulrahaman Mu’azu Dan Jabalu ya ce sakacin gwamnatin jihar Sokoto ne ya jawo masu wannan mummunar asara domin babu hukumar kashe wuta, domin a cewar sa da ankawo hukumar ta kawo dauki da an shawo kan gobarar.

A daya bangaren kuma, wasu daga cikin masu shagunan sun dora laifinne akan jami’an tsaron da suka tare su, da hana su kaiwa ga shagunansu tun kafin wutar ta kaiga kama masu shaguna.

Duk da shike babu tabbacin sanadiyyar gobarar, jama'a da dama sun alakanta ta da wutar lantarki.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna daga Sokoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG