Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Lakume Kayan Abincin Da Ake Baiwa 'Yan Gudun Hijira


Gobara ta lakume kayan abinci a kasar Yemen wanda hakan ya durkusad da ayukan jin kaia wannan kasar.

Mummunar gobara ta barke a wurin da hukumar abinci ta duniya ke ajiye kayan abinci a Yemen, a kusa da gefen tekun Bahar Al-Ahmar dake birnin Hodeida.

Kafan yada labarai mallakar gwamnatin kasar ta Yemen ta bayyana cewa gobarar wadda ta fara jiya asabar tayi mummunar barna musammam ga kayayyakin aikin jin kai da aka tara a wannan wuri, sai dai kawo yanzo ba a gane abinda ya haddasa wannan gobarar ba.

Wani jamiin Gwamnati ya shaidawa wa kanfanin dillacin labarai na Faransa cewa gobarar ta lakume manya-manyan runbunan ajiye abinci guda hudu,wanda ke dauke da tarin kayan abincin da yakai tan 50.

Jamiaan kasar taYemen sun bukaci MDD data binciki wannan al’amari.

Haka kuma ko baya ga kayan abinci dake jibge a cikin wadannan runbunan akwai katifu, da dai sauran kayayyakin anfanin bani adama da ake rarrabawa bayin ALLAH da yaki ya raba su da muhallin su.

Yemen dai ta shiga cikn halin oni ‘yasu ne a cikin wannan lokacin tun daga cikin shekarar 2015 lokacin da kasar Iran take mara wayan tawayen Shia’a baya, yayin da ita kuma kasar Saudiyya ke goyon bayan rundunar hadin gwiwa wanda kasashen duniya suka yarda da halarcin su.

Shi dai wannan gari na Hodaida nan ne runbunan abinci da kayayyaki suke yana tamkar matsayi wani ruhin kasar ta Yemen ne, domin da yawan ‘yan kasar suna dogaro ne da abincin da ake rarraba musu daga wannan wurin.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG