Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobarar Bututun Mai Ta Tilasta Rufe Tashar Wutar Lantarki a Najeriya


Babatunde Fashola, ministan ayyuka, makamashi, da gidaje na Najeriya

Gobarar da ta tilasta rufe tashar samar da wutar lantarki ta kara dagula sha’anin ayyukan sarrafawa da ma wasu al'amuran kasuwanci a kasar da ta dade tana fama da karancin wutar lantarki

Wata gobarar da ta faru a wani bututun man gas a Najeriya, ta haddasa tsinke wutar lantarki a duk fadin kasar, a cewar ma’aikatar makamashi ta Najeriya a yau laraba.

Sanarwar ta kara fitowa fili da irin matsalar da kasar ke fuskanta game da samun isasshiyar wutar lantarki da kasar ke bukata a ma’aikatu da gidaje.

Sau tari akan dorawa tashar laifin samar da wuta mai dorewa, lamarin dake takurar da ci gaba a kasar da ta fi kowace kasar Afrika yawan al’umma da girman tattalin arziki, duk da kokarin da aka yi a saka hannun ‘yan kasuwa cikin lamarin.

Yawancin ma’aikatu da gidaje suna samar ma kawunansu wutar lantarki ne ba tare da yin la'akari da tsadar yin hakan ba. Su kan yi anfani da mai ne a shirin ko ta kwana ganin yadda ake yawan dauke wuta a kasar.

Gobarar da ta samo asali daga bututun mai na Escravos-Lagos dake kusa da garin Okada a jihar Edo, ta janyo katsewar man gas ga tasoshin samar da wutar lantarki da dama, a cewar ma'aikatar.

Katsewar samar da wutar lantarki a tasoshin, a saboda katsewar iskar gas da suke samu, ta sa babban layin kai wutar lantarki zuwa sassan kasar ya daina aiki da karfe 8 da minti 20 na daren talata, 2 ga watan Janairu.

Ma'aikatar ta ce Najeriya na samun akasarin wutar lantarkinta ne daga tasoshin samar da wutar lantarki masu aiki da man gas.

Sai dai bayan aukuwar gobarar ma’aikatar makamashi ta ce ana aiki dare da rana kan bututun da wutar ta shafa kuma da zarar an kammala aikin za’a sake bude tashar ta ci gaba da ba da wuta.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG