Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobarar Dajin dake Ci a Jihar California Sai Fadada ta Keyi


Wasu gidajen da gobarar ta lakume

Yayinda gobara dake ci a arewacin jihar California ke fadada, da alamu alamura zasu kara rincabewa yau Alhamis saboda isak da za'a yi da ka iya kawo cikas ga ayyukan 'yan kwana kwana

Gobarar dajin dake ake fama da ita a Arewacin jihar California ta Amurka, ta ci gaba da fadada a jiya Laraba, lokacin da iska ke kara rura wutar, abinda ya tilastawa jami’ai kwashe mutanen dake yankin wutar.

Masu hasashen yanayi sunce a yau Alhamis za a samu karin iska mai karfi yankin Arewacin California, wanda zai sa duk wani kokarin shawo kan wutatai har guda 22 dake ci a Arewacin birnin San Francisco, ya fuskanci wahalar samun nasara.

Jami’ai sunce izuwa yanzu mutane 21 ne suka mutu wasu kuma sama da 300 an neme su an rasa duk a dalilin gobarar. Layikan wutar lantarki da suka fado na ci gaba da kasancewa akan titunuan unguwannin da wutar ta lakume, yayin da ‘yan kwana-kwana ke kokarin kashe gobarar.

‘Yan Sanda sun rufe hanyoyi masu yawa domin hana mutane shiga yankunan da gobarar ta lalata, wadanda suka hada da hekta dubu 69 a cikin yankunanb kananan hukumomi da daman a jihar

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG