Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobarar Daji Ta Kashe Akalla Mutane 10 a Jihar California dake Amurka


Gobarar daji a California

Kowace shekara jihar California ta kan yi fama da gobarar daji amma ta wannan shekarar ta yi muni saboda gobarar ta lakume gidaje da wuraren kasuwanci sama da 1500 baicin mutuwar mutane 10

A kalla mutane 10 ne suka mutu yayin da gobarar daji ke ta kone wani yanki na jihar California ta Amurka, a cewar shugaban ‘yan kwana-kwana jiha Litinin.

Ofishin ‘yan sandan garin Sonoma ya kafe a Twitter cewa an samu rahotan mutuwar mutane bakwai a dalilin gobarar.

Gobarar dai ta lakume gidaje da wuraren kasuwanci sama da 1,500 yayinda mutane da yawa suka raunata, wasu kuma ba a san inda suke ba, duk a sanadin tashin wutatai kashi-kashi har 14 a cikin wasu kananan hukumomi uku dake Arewacin jihar California.

An dai samu kwashe mutane dubu ashirin, ciki har da daruruwan marasa lafiya daga asibitocin yankin.

Ma’aikatar kare gandun daji ta California ta ce an fara binciken abin da ya haddasa tashin gobarar.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG