Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gocewar Laka a Afghanistan


​'Yan sandan Afghanistan sun yi harbi a iska jiya Talata don tarwatsa wasu kauyawa da ke neman kayan tallafi a inda aka sami wata mummunar gocewar tudu a arewa maso gabashin kasar.

Hukumomi sun ce babu wanda ya sami raunuka yayin da wasu mutane da dama su ka ruga wajen wata tirela mai dauke da kayan agaji ga wadanda gocewar tudun ta makon jiya ta rutsa da su.

Gocewar tudun ta binne daruruwan mutane a kauyen Abi Barik da ke lardin Badakhshan lokacin da wani bangare na wani babban tsauni ya balle bayan wani ruwa kamar da bakin kwarya da aka yi. Mutane akalla 2000 sun rasa muhallansu a wannan hadarin wanda na daya daga cikin mafiya muni da aka taba yi a Afghanistan.
XS
SM
MD
LG