Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GOMBE: Ali Kwara Da 'Yan Sanda Sun Cafke Wasu Barayi


Wasu 'yan sandan Nijeriya a bakin aiki

A jihar gombe wasu ‘yan fashi da makami sun hallaka wata mata ‘yar kasuwa ‘yar kasar kamaru sa’an nan suka kuma harbe wani malamin jami'ar garin kashere dake jihar gomben a lokacin dasuke tafiya a cikin motoci a kan hanyar gombe zuwa yola.

A cewar mai Magana da yawun jami’an ‘yan sandan jahar DSP Ahmed Usman, matar mai suna Zainab Mamuda ‘yar kasuwa ce kuma ta fito sayayya ne daga Kano akan hanyarta ta komawa kasar su sai ‘yan fashin suka tare motar da take ciki wadda ta rasa ranta a sanadiyyar harbin da suka yi.

Wani mutum da shima ya rasa ransa a cewar kakakin hukumar ‘yan sandan shine wani malamin jami’a mai suna Umar wanda suka hallaka kuma suka kwashe wayoyinsa na hannu.

Kakakin ya kara da cwa wadannan ‘yan fashi su kimanin guda takwas na dauke da makamai da sannduna, kuma a lokacin da ‘yan sanda suka isa wajan da lamarin ya faru, ‘yan fashin sun gudu.

A wata sabuwa kuma hukumar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wasu Fulani dake aikawa jama’a rubutaccen sako mai barazanar kisa idan ba’a biya masu bukatar sub a kamar yadda DSP Ahmed ya bayyana.

Ya ce “da taimakon sanannen maharbin nan Ali Kwara, mun yi nasarar cafke wasu matasa su uku wadanda suka kitsa wani yunkuri domin sace mahaifin su inda suka rubuta masa wasika ba tare da yasan cewar ‘ya’yan sa ne suka rubuta ba suka bukaci ya basu kudi Naira miliyan guda ko kuma su hallaka shi.

Koda shige bincike ya nuna cewar mutumin ya je ya sayar da shanunsa guda shidda ya sami kudi Naira dubu dari biyar ya kai masu, kawo yanzu dai suna hannu kuma biyu daga ciki ‘ya’yan cikin sa ne dguda daga ciki kuma makwabcin sa.

Ga cikkaken rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG