Accessibility links

Goodluck Jonathan Zai Bude Taron Habbaka Tattalin Arzikin Arewa Maso Gabas


Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaba Goodluck Jonathan shi ne zai bude taron habbaka tattalin arzikin arewa maso gabashin Najeriya da za'a fara ranar uku ga watan Disamba a birnin Gombe babban birnin jihar Gombe

Ranar uku ga watan Disamba za'a fara taron habbaka tattalin arzikin arewa maso gabashin Najeriya da jihar Gombe ta dauki nauyin shiryawa yayin da shugaban kasar Goodluck Jonathan zai bude taron.

Shugaban kwamitin dake shirya taron Malam Mohammed Kabiru Ahmad shi ya bayyana hakan cewa jihar Gombe ita zata dauki bakuncin taron kana shugaba Jonathan zai kaddamar da bude taron ranar Talata mai zuwa. Arewa maso gabashin Najeriya dai ta kunshi jihohi shida wato Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe. To ko menene shiyar zata nuna wa kasar da ma duniya gaba daya? Shugaban shirya taron ya ce akwai abubuwa da yawa da suka yi. Sun buga wani littafi da ya bayyana wuraren da masu saka jari zasu iya saka jari. Arewa maso gabas Allah ya albarkaceta da filayen gona da dabbobi da ma'adanan kasa. Ya ce akwai wadanda zasu zo daga kasashen China da Ukraine da Australia da wasu kasashen duniya. Idan sun zo zasu nuna masu fannoni daban daban da zasu iya saka jari kuma su zasu taimakesu su yi hakan. Ya ce zasu zauna dasu su tattauna su ga ta yaya za'a taimakawa juna.

Dangane da kananan 'yan kasuwa ya ce sun gayyacesu ta hannun cibiyar kasuwanci ta kasa wato CIMA a takaice. Ya ce taron babban taro ne amma yana fata zasu samu zarafi su gana da kananan manoma da kananan 'yan kasuwa. Domin taimakawa kananan 'yan kasuwa ya ce sun gayyato gwamnan babban bankin Najeriya ya wayar da kawunan mutane dangane da taimakon da ake yiwa kananan 'yan kasuwa. A nuna masu yadda karamin dan kasuwa zai iya samun lamuni da zai iya habbaka harakar kasuwancinsa.

Malam Mhammed Kabiru Ahmad ya ce akwai abubuwa da suka yi domin su tunkari komabayan da shiyar ke fama da shi a fannin tattalin arziki. Na farko sun yi nasu taron domin su tantance bukatun kowace jiha a fannin noma da ilimi. Abu na biyu shi ne yin nazari kan abun da ya kamata a yi bayan taron.

Sa'adatu Mohammad Fawu nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG