WASHINGTON, DC —
A wannan shirin, mahaifiyar karamin yaron da tayi zargin an yi mashi fyade da gasa mashi akuba a makarantar kurame ta gwamnati dake Kuje, Abuja tace hukumomi sun yi watsi da batun suka nemi zarginta da kage da neman yin damfara.
Saurari bayanin nata
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.