Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Fulani Na Kokarin Hana Matansu Tallar Nono, Janairu 17, 2019,


Grace Alheri Abdu

A bana Shirin Domin Iyali zai fara tashi ne da batun yunkurin inganta sana’ar saida nono da Fulani mata suka gada kaka da kakanni, sana'ar da wadansu magidanta Fulani suka fara bayyana damuwa a kai, tare da barazanar daukar mataki kan wanda ya ci gaba da wannan sana’ar

Wannan ya biyo bayan zargin da wadansu Fulani ke yi cewa, wadansu mata suna shiga ayyukan assha a lokacin gudanar da wannan sana’ar, sabili da haka suke neman daukar matakin kare mutuncin Fulani.

Wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari ya hada rahoto na musamman kan wannan batun, a matsayin shinfida a bibiyar da zamu fara mako mai zuwa kan batun.

Saurari korafin fulanin.

Fulani Na Kokarin Hana Matansu Tallar Nono-10:30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:32 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG