Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guguwar Irma ta ragargaza sassan Haiti da Dominka, kuma za ta doshi Cuba da Bahamas


Wani sashin St. Matin yayin da mahaukaciyar guguwar Irma ke kadawa tun ma a ranar Larba.
Wani sashin St. Matin yayin da mahaukaciyar guguwar Irma ke kadawa tun ma a ranar Larba.

Guguwar Irma, wadda ta bullo bayan guguwar Harvey, ita ,ma ta fara mummunar barazana. Tuni ma wasu himman wurare su ka fara salwanta a Haiti da Janhuriyar Dominika sanadiyyar mahaukaciyar guguwar ta Irma.

Mahaukaciyar guguwar nan ta Irma na kan bararraka yankunan Haiti da Janhuriyar Dominica da ruwa da iska mai tsanani, amma an yi sa'a saboda ga dukkan alamu guguwar ba ta abka masu kai tsaye ba.

Masu hasashen lawalin guguwa sun ce 'zuciyar' guguwar za ta ratsa ta Hispanola - tsibirin da yayi kan iyaka da kasashen biyu -- da kuma tsibirin Turks da Caicos da daren jiya Alhamis kafin kuma ta doshi Cuba da Bahamas.

Har yanzu masu hasashen na cewa cewa guguwar na da abin da su ka kira, "matukar hadari" kuma ta kai mataki na 5 a ma'aunin guguwa, inda ta ke kadawa da iska mai gudun kilomita 280 a sa'a guda.

A halin da ake ciki kuma, guguwar ta Irma mai cike da hadari, ta tilasta kamfanonin jiragen sama soke tafiye-tafiye har sama da 4,000 na zuwa da kuma tashi daga filayen jiragen saman Caribbean da kuma Florida a cikin ranaku tara na farko a watan Satumba. Kwararru a dandalin 'intanet' na FlightAware.com sun ce adadin ma na iya lkaruwa yayin da guguwar ke dosar Florida, inda filin jirgin saman kasa da kasa na Miami ya ke, wanda ya na daya daga cikin filayen jiragen sama mafiya hada-hada a duniya. Kowace rana jiragen sama wajen 106 na sauka da tashi sau 1,200 a Miami, zuwa wurare wajen 150.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG