Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gurbatacciyar Iskar Cikin Gida Na Kashe Mutane Sosai


Gurbacewar iska

A wani labari mai bayar da mamaki, hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce anfi samun illar gurbatacciyar iska a gida fiye ma da masana'antu da zirga-zirgar motoci.

Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) ta ce cikin mutane 10, guda 9 na shakar gurbatacciyar iska, kuma gurbatacciyar iska ta cikin gida, wadda ba a cika ganewa ba, ita ce ta fi illa.

Rahoton na baya-bayan nan na WHO ya ce gurbaciwar iska na kashe mutane miliyan 7 a kowace shekara, kuma al'ummomin da ke fama da matsatsi a Afurka da Asiya sun fi cutuwa.

"Wannan babbar matsala ce da ba za a lamunta da ita ba," a cewar jami'ar hukumar ta WHO Dr. Maria Neira.

Gurbatacciyar iska, a cikin gida ko waje, duk kan kai ga bugun zuciya ko cutar zuciya ko cutar huhu da kuma muguwar cutar nan ta numfashi wato asthma.

A yayin da akasarin mutane su ka fi danganta gurbacewar iska da tururi da hayakin da ke fitowa daga masana'antu da motoci, rahoton na WHO ya nuna cewa gurbacewar iskar cikin gida na sanadin mutuwar mutane wajen miliyan 4 a duk shekara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG