Gwajin allurar cutar corona ya zo da wata ‘yar fa’ida to amma kuma da wani abin takaici a gwajin farko a maganin, bisa ga bayanin wani nazari da aka buga a jiya Jumma’a a mujallar harkokin lafiya mai suna The Lancet.
Maganin, wanda aka gwada a kasar China, ya zaburar da garkuwar jiki ga akasarin majinyatan, to amma ba duka ba, kuma da damansu sun samu illa.
(Gwajin mutane a Wuhan, inda cutar corona ta samo asali a China)
Sakamakon wannan binciken ne aka fara wallafawa game da gwajin farko na wannan magani na COVID-19. Akwai kuma wasu karin magunguna wajen 100 a fadin duniya da ake kan ingantawa, ciki har da wasu guda 9 da aka fara gwada su a asibiti.(Wasu ma'aikatan asibiti a birnin Wuhan, inda cutar corona ta samo asali a kasar China)
“Da ace shi ne kadai maganin da ake da shi, ina ganin mutane da dama za su sha,” a cewar Gary Simon, shugaban sashin nazarin cututtuka masu yaduwa a Jami’ar George Washington da ke birnin Washington D.C.
Ya ce saidai kuma, “babu yadda wannan maganin zai samu shiga sosai muddun ba su kara inganta shi ba.”
Facebook Forum