Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwajin Makaman Da Koriya Ta Arewa Ke Yi Na Barazana Ga Duniya


Wani makamin koriya ta arewa
Wani makamin koriya ta arewa

Duniya na dada sa ido kan gwaje-gwajen makamai da Koriya Ta Arewa ke yi. An kuma bayyana yankin Pacific da cewa shi ya fi fuskanar barazana.

Gwajin makami mai linzami da kasar Koriya Ta Arewa ta yi na baya-bayan nan wata babbar barazana ce ga yankin Pacific da ma duniyar baki daya, a cewar kwamandan harkokin soji na NATO.

Koriya Ta Arewar ta gwada harba makami mai linzamin ne daga jirgin karkashin ruwa da daren ranar Jumma'a a kusa da gabar birnin Sinpo mai tashar jirgin ruwa. Bayanai na farko na nuna cewa makamin ya fadi a Tekun Japan, a cewar kwamandan sojin Amurka, wanda ya bi diddigin yadda aka gudanar da gwajin. Kafar labaran Koriya Ta Kudu ta Yonhap ta ce injin din makamin ya kama da wuta, to amma makamin ya tarwatse ne da tazarar kilomita 10 a sararin sama. Irin wannan gwajin da aka yi a watan Afirilun da ya gabata ma bai yi nasara ba.

"Kim Jong Un da gwamnatinsa na cigaba da ingantawa da kuma gwajin makamai masu linzami, kuma bayan duk wani gwaji su kan kara ingantawa, su na warware matsalolin baya," a cewar babban kwamandan NATO, Janar din Amurka Curtis M Scaparrotti mai kula da bangaren Turai, a hirarsa da 'yan jarida a wuirn babban taron NATO a birnin Warsaw jiya Asabar.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG