Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Abba Yusuf Ya Kafa Harsashin Ginin Gadar Saman Da Zata Ci Naira Bilyan 15 A Kano


Abba gida gida
Abba gida gida

A kokarinsa na maida birnin Kano zuwa katafariyar alkarya, tare da rage mata cunkoson ababen hawa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dora harsashin ginin gadar sama mai hawa 3 da zata lakume Naira biliyan 15 a Kofar Dan Agundi.

A ziyarar da yakai wurin da za’a gina gadar a jiya Lahadi, gwamnan bisa rakiyar mukarrabansa, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na sauya taswirar birnin Kano.

Ya kuma jaddada mahimmancin inganta zirga-zirgar ababen hawa a kokarin daga likkafar Kano zuwa katafaren birnin.

Kwangilar aikin, wacce aka baiwa kamfanin gine-gine na “CCG Nigeria Limited” a watan Disambar daya gabata, nada wa’adin kammalawa na watanni 18. Kuma wani bangare ne na wani sahihin aikin tsara birane da zai hada da wata gadar saman a shatale-talen tal’udu, wanda aka tsara domin takaita cunkoson ababen hawa.

A cewar gwamnan, “mun kirkiri hanyoyin kewaye, kuma muna sa ran masu ababen hawa suyi biyayya ga ka’idojin kiyaye afkuwar hadura tare da kyale aikin gadar ya gudana cikin lumana.”

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature, ya fitar tace, samarda ababen more rayuwa da inganta bangaren ilmi, sune bangarorin da gwamnatin Kano mai ci tafi maida hankalinta akai.

A cewar sanarwar, hakan ya sake bayyana aniyar gwamnatin Abba Yusuf ta sauya fasalin birnin Kano zuwa alkaryar data dace da zamani.

Da yake amsa tambayoyin bayan bikin kaddamar da aikin ginin gadar, manajan ayyuka na kamfanin “ccg nigeria limited”, Gee Wang, ya bayyana kwarin gwiwar kammala aikin cikin wa’adin da aka diba.

A cewar wang, “mun kudiri anniyar kammala aikin cikin wa’adin da aka diba, tare da bada tabbacin shigar da aikin cikin taswirar birnin kano ba tare da wata matsala ba.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG