Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Akeredolu Na APC Ya Lashe Zaben Ondo


Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu (Hoto: Twitter @RotimiAkeredolu)
Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu (Hoto: Twitter @RotimiAkeredolu)

Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya yi nasarar samun wa'adi na biyu bayan da hukumar zabe ta INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben jihar da aka yi a karshen mako.

Akeredolu wanda ya yi takara karkashin jam’iyyar APC, ya samu nasarar lashe 15 daga cikin kananan hukumomi 18 da ke jihar wave ke kudu masa yammacin Najeriya.

Gwamnan ya samu kuri’a 292, 830 yayin da abokin hamayyarsa Eyitayo Jegede na jam’iyyar adawa ta PDP ya samu kuri’a 195, 791.

Bayanai sun yi nuni da cewa mataimakin gwamna Agboola Ajayi da ya yi takara karkashin jam’iyyar ZLP ya samu kuri’a 69,127.

Zaben na ranar Asabar ya gudana ne kasa da wata guda bayan wanda aka yi a jihar Edo a kudu maso kudancin Najeriyar, wanda PDP ta lashe.

'Yan takara 17 ne suka kara a zaben da suka hada da gwamna mai-ci Rotimi Akeredolu na jam’iyyar APC, da EyitayoJegede na Jam’iyyar PDP da kuma Agboola Ajayi na jam’iyyar ZLP da suka kalaubalance shi.

Akwai dai rahotanni da ke nuna cewa wasu jam'iyyu na zargin an tafka magudi a zaben.

A zaben 2016, gwamna Akeredolu na APC da Mr. Ajayi na jam’iyyar Zenith Labour Party, (ZLP) wanda shi ne mataimakin gwamna Akeredolu, sun ka da Mr Jegede na jam’iyyar PDP.

Amma Ajayi, ya raba gari da gwamna Akeredolu inda ya sauya sheka ya koma ZLP a wannan zabe don kalubalantar tsohon maigidansa.

Wannan shi ne karo na biyu da manyan jam’iyyun kasar biyu, wato APC da PDP suke gwada farin jininsu a zaben jihohi wanda wasu masu fashin baki ke cewa zai iya zama manuniya ga abin da zai faru a zaben 2023.

A ranar 19 ga watan Satumba, gwamna mai ci Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP ya lashe zaben jihar ta Edo bayan da ya kada abokin karawarsa Osagie Ize-Iyamu na APC.

Saurari cikakken rahoton Hassan Umaru Tambuwal wanda ya tattaro ra'ayoyin wasu mazauna jihar ta Ondo:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG