Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Lamido Ya Mayarda Martani Kan Ficewar Obasanjo daga PDP


Sule Lamido gwamnan Jiigawa

Ficewar tsohon shugaban Najeriya Chief Olusegun Obasanjo daga PDP ta tada kura.

Inji gwamna Lamido shi Obasanjo shugaba ne wanda ya shugabanci kasar a zamanin mulkin soja da kuma lokacin da aka kafa jam'iyyar PDP. Yace kowane dan adam yana da nau'i na fushi da kuma na murna, abun da yayi nuna fushi ne kawai

Shugaba Obasanjo yayi yakin hadin kan Najeriya. Shugaban dake ci yanzu dansa ne. Shi ya kawoshi. Sabili da haka da da uba, wato Jonathan da Obasanjo akwai hakin kasa akansu. Duk fushin da Obasanjo zai yi da dansa, kome ya faru dansa ne. Shi kuma da ko menene uban yayi da shi yake gani ba daidai ba ne babu abun da zai yi.

Gwamna Lamido yace gaskiya asiyasance Obasanjo uba yake garesu amma kuma akwai hakin shugabanci akansa cewa komai wuya, komai masifa komai fushi ana tsanmanin babba ya san irin fushin da zai yi. Obasanjo ubansu ne kuma ba zasu gujeshi ba. Haka ma shi Jonthan da yake gareshi babu abun da zai iya yi sai dai Allah ya sawaka..

Dangane da ko zasy je su lallashi Obasanjo sai gwamna Lamido yace idan babba yayi fushi akwai hadari. Yace yanzu mutanen kudu suna gud daga arewa suna komawa kudu. Haka ma mutanen arewa suna gudu daga kudu suna komawa arewa. Wannan lamarin yana da ban tsoro. An shiga wani yanayi yanzu saidai manya su kara yin hakuri su kai fushinsu nesa. Abun da za'a sa gaba yanzu shi ne yaya za'a gyara kurakuran yara da aka kawo shugabanci. Obasanjo shi ya kawo Jonathan ba da dominsa ba Jonathan bai isa ya zama shugaban Najeriya ba ko ya mulketa.

Keta katin zama dan jam'iyyar PDP a bainar jama'a ba zai yi maganin komi ba kuma ba shi ne mafita ba. Nuna fushinsa a bainar jama'a bai kawar da gaskiyar cewa shi ne ya kawo Jonathan a siyasance ba.

Gwamna Lamido yace korar da PDP tace ta yiwa Obasanjo bayan ya fice wauta ce. Duk wadanda suke PDP yanzu 'ya'yansa ne.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG