Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Jonathan Kada Yarda A Yi Amfani Da Kai Wajen jefa Jihar Taraba Cikin Rikici-Inji Kungiyar Hada Kan Al'umar Jihar Taraba.


Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai
Daga jihar Taraba kuma, kungyar hada kan al’umar yankin tayi kira ga shugaba Goodluck Jonathan kada ya bari a yi amfani da shi wajen jefa jihar cikin rikici.

Ana zargin wadanda suke neman amfani da gwamnan sun saci jiki sun dauke shi zuwa Abuja, domin nunawa mahukuntan kasar cewa ai gwamnan ya sami lafiya, kuma yana shirin ya koma bakin aiki. Amma wakilan majalisar dokokin jihar, da kungiyoyin jihar suka ce ko kusa ba zasu yarda da haka ba.

Kungiyar wacce ta kira taron manema labarai ta bayyana damuwar kan yadda wadanda suke so su yi amfani da rashin lafiyar gwamnan jihar Danfulani Baba suntai domin biyan bukatar kansu. Ga Ibrahim Abdulaziz da ci gaban rahoton
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG