Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Bayelsa Ya Kebewa Fulani Makiyaya Katafaren Filin Kiwo Kyauta


Fulani Makiyaya
Fulani Makiyaya

Ta bakin Kabiru Muhammadu Shittu shugaban Fulani makiyaya dake jihar Bayelsa yace gwamnan ya kirashi a matsayinsa na shugaba ya gaya masa cewa ya kebe filin kiwo kimanin kadada dubu daya da dari biyu domin kiwo kyauta ba sai sun biya ba.

Aikin shugaba Shitu shi ne kula da makiyaya da manoma domin kada su yi fada da juna. Gwamnan ya kafa kwamiti wanda shi Shittu shi ne shugaba.Gwamnan ya yi haka ne da shaidar duk shugabannin jami'an tsaro dake jihar. Gwamnan ya fada baya son abun da zai kawo sabani tsakanin mutanensa da makiyaya.

‘Yayan Fulani masu kiwo
‘Yayan Fulani masu kiwo

Wai gwamnan ya nada kwamitin ne domin ya nunawa Najeriya cewa ana iya zama lafiya da juna.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

XS
SM
MD
LG