Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Borno Ya Jajantawa A'ummar Jihar Kan Tashin Bamabamai


Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima.

Gwamnan Borno Ibrahim Kashim Shettima ya jajantawa al'ummar jihar musamman 'yanuwan wadanda suka rasa rayukansu ko suka jikata sanadiyar tashin bamabaman ranar Lahadi da ta gabata

Bamabaman sun yi sanadiyar mutuwar mutane hamsin da hudu mutane fiye da saba'in ne kuma suka jikata.

Gwamnan ya zagaya unguwannin da bamabaman suka tashi inda ya yiwa jama'a jaje da kuma yiwa wadanda suka rasa 'yanuwa ta'a ziya.

Gwamnan ya je asibitin Umaru Shehu inda ya ga masu jinya sakamakon raunukan da suka samu daga tashin bamabaman. Nan take gwamnan ya yi alkawarin biyan kudin jinyarsu.

Gwamnan yace ya ji takaicin abun da ya faru amma da yaddan Allah irin wannan haukar ta zo karshe saboda kudurin shugaban kasa na ganin an dakile ta'adanci..

Gwamna Shettima ya gargadi jama'a da su shaidawa jami'an tsaro da zara sun ga wanda basu yadda dashi ba.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG