Accessibility links

Gwamnan Jihar Kaduna Patrick Yakowa Ya Rasu


Marigaryi Gwamnan jihar Kaduna Patrick Yakowa a cikin shudiyar riga
Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da rasuwar gwamnan jihar Kaduna Patrick Yakowa da kuma tsohon mai baiwa shugaban kasa shawarwari kan harkokin tsaro janar Owoye Azazi, sakamakon hadarin jirgin helicofta da ya auku a kauyen Nambe na jihar Bayelsa inda suka je domin halartar jana’izar mahaifin Oronto Dauglas daya daga cikin mukarraban shugaba Goodluck Jonathan.

A cikin hirarsa da Sashen Hausa Rev Joseph Hayeb daya daga cikin masu ba marigayi Patrick Yakowa shawarwari kan harkokin addini ya bayyana cewa, gwamna Yakowa ya tashi daga Kaduna zuwa Patakwal a wani jirgi dabam kafin daga wurin suka shiga karamin jirgi zuwa Nambe inda aka yi jan’izar.

Bayan jana’izar ne janar Azazi ya gayyaci Mr. Yakowa da dogarinsa su shiga jirgi mai saukar angulu na mayakan ruwa da zai koma a ciki kasancewa akwai sauran kujerun mutum biyu. Tashinsu ke da wuya kan hanyarsu zuwa tashar jirgin sama ta Patakwal dake tazarar tafiyar kimanin minti 18 hadarin ya auku, nan da nan bayan kuccewar jirgin ya kama da wuta abinda ya sa aka gaza kai dauki.

Fadar shugaban kasa ta Najeriya ta bayyana takaicin rashin. Ta kuma bayyana sunayen sauran wadanda suka rasa rayukansu a hadarin da suka hada da dogarin janar Azazi Mohammed Kamal, da dogarin gwamna Patrick Yakowa Dauda Tsoho da kuma matukan jirgin Murtala Mohammed Daba da Lt. Adeyemi O. Sowole

Shugaba Goodluck Jonathan ya aika ga sakon ta’aziya ga dangi da abokai da gwamnatoci da kuma illahirin al’ummar jihohin Kaduna da Bayelsa ya kuma bada umarnin bincika masababin hadarin.
XS
SM
MD
LG