Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar Maradi a jamhiruyar Niger, ya ziyarci garin da makiyaya da Fulani suka yi fada


 Jandarmomin Niger
Jandarmomin Niger

Taho mu gama da Fulani makiyaya da manoma suka yi a garin Debi wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku ya sa gwamnan jihar Maradi kai ziyarar jajantawa garin

Bayan fadan da ya faru a garin Debi cikin jihar Maradi mutane uku suka rasa rayukansu har da sarkin garin. Sai dai tuni wanda ya kashe sarkin ya mika kan sa ga hukuma

Gwamnan jihar Maradi Alhaji Zakari Umaru ya ziyarci garin kuma ya yi jawabi. Yace “ duk jama’ar Maradi suna yi maku ta’aziya”. Ya yi fatan Allah ya kwantar masu da hankali bisa abun da ya faru.

Sai dai gwamnan ya nuna damuwarsa yadda mutanen garin suka maida martini fiye da abun da aka yi masu. Yace bin doka shi ne abu na fi a’ala domin idan ba’a bin doka babu wanda zai rayu. Yana mai cewa su da suke shugabanci doka ta basu iko amma akwai yadda za su yi anfani da ikon da suke dashi. Idan an zalunci mutum cewa aka yi a kai kara wajen hukuma ba mutum ya aiwatar da nashi hukumcin ba, inji gwamnan. A cewarsa zasu bari doka tayi aikinta.

Ofishin ministan cikin gida na jamhuriyar Niger ya fitar da wata sanarwa inda ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG