Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar Niger Ya Bayyana Takaicin Sa Bayan Ya Ziyarci Gidan Yari.


NEJA: GWMNAN JIHAR NEJA Alhaji Abubakar Sani Bello

Gwamnan jihar NigerAlhaji Abubakar Sani Bello yace bai dace a ajiye mutane gidan yari ba tare da yanke musu hukunci ba akan lokaci.Gwamnan yana magana ne sailin da ya ziyarci gidan yarin garin Kontagora

Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya bayyana takaicin hukuncin da aka yankewa wasu mazauna gidan yari da suka aikata kananan laifukka.

Gwamnan Abubakar Sani Bello ya bayyana takaicin ne sai’lin da ya kai ziyara a gidan yarin garin Kontagora dake cikin jihar ta Niger.

Gwamnan jihar ta Neja yace bai dace ana cusa mutane gidan yari na tsawon lokaci ba, ba tare da an yanke musu hukunci ba.

Yace yaga wadanda suka dauki shekara da shekaru gidan yarin ba tare da yanke musu hukuncin laifukkan da suka aikata ba.

Gwamnan yace wasu sun yi shekaru 4, wasu 2, wasu ko har shekaru 6 da sunan jiran hukunci, abinda yace wannan bai dace ba.

Da Wakilin Muryar Amurka Mustapha Nasiru Batsari ya tambaye shi ko akwai wadanda zasu ci gajiyar wannan ziyar tasa, sai Gwamnan yace, kwarai da da gaske kuwa.

Ga Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani2'59

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG