Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Legas Ta Umurci Jami'an Kula da Motoci VIO da Hukumar Kiyaye Hadari Su Bar Titunan Jihar


Gwamnan Legas Akinwumi Ambode

Daga yau jami'an kula da motoci da aka sani da suna VIO zasu bar titunan Legas har abada kana hukumar dake kiyaye haduran motoci ,wato FRSCN zasu kwashe nasu i-nasu su koma gefen manyan tituna na gwamnatin tarayya

Tun ba yau ba direbobi da masu anfani da hanyoyi, musamman a jihar Legas, suke zargin jami'an VIO da hana ruwa gudu wajen haddasa hadura maimakon hanasu aukuwa tare da zarginsu da cin hanci da rashawa inda suke karban na goro a hannun direbobi.

Matakin da gwamnan jihar ta Legas ya dauka ya farantawa da yawa cikin masu anfani da titunan jihar rai. Sun dora alhakin cunkoson da ake samu da motocin haya akan jami'an VIO.

Wani cewa yayi Allah ya raka taki gona domin babu abun da suke tsinanawa mutane illa kawai cunkoso tare da kutuntawa jama'a. Yakamata dama a hanasu.Wani ya ce babu abun da suke yi illa haddasa dogon layin motoci suna hana tafiya lamarin dake kawo tsaiko ga harkokin yau da kullum..

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG