Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Bata Biya Diyya ba Akan Samarda Wutar Lantarki


Madatsar Ruwa don Samarda Lantarki
Madatsar Ruwa don Samarda Lantarki

Alumomoin dake zaune a yankin madatsar ruwan Zungeru, a jihar Neja, da Gwamnatin tarayyar Najeriya, keyi da nufin samarda tashar wutar lantarki, mai karfin Mega Watt dari bakwai na ci gaba da kokawa saboda yanda suka ce har yanzu ba’a biya su hakoki na garuruwa da gonakin su da aka tayar a sakamakon wannan aiki ba.

Ko a baya ma dai wadannan alumomi, sunyi wani yunkuri na dakatar da Kamfanin dake gudanarda wannan aiki saboda korafin rashin biyan su hakokin su.

Shugaban kungiyar alumomin da yakin na madatsar ruwan na Zungeru, Alhaji Adamu Garba, yace sun yi korafi dagane da neman a biya su hakin har zuwa ga fadar Sarkin Minna, wanda ya hada da taruruka har tsawon shekaru biyu, amma har yanzu bata sake zani ba.

Wakilin muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari, yayi kokarin jin ba’asi daga sarkin Minna ko kuma masarautar amma hakan bai samu ba.

Madatsar Ruwa - 2'57"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

XS
SM
MD
LG