Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Gwamnati Na Wasa Da Hankalin Mu"-Inji Al'ummar Nijar


Wata sabuwar Mahawara ta barke tsakanin 'yan kasar Nijar tun bayan da gwamnatin kasar ta fitar da wata sanarwa game da wadanda suke da hannu a badakalar ma'aikatar tsaron kasarta Nijar.

Biyo bayan sanarwar da gwamnatin Nijar tayi, mataki da hukuncin da ta ayyana zata dauka kan duk wanda aka samu da hannu cikin wannan badakalar, al’ummomin Nijar suna ta bayyana ra’ayoyinsu akan wannan al'amari.

Inda mafi akasarin al’ummar kasar suka nuna rashin amincewarsu da matakin da gwamnati ta ce zata dauka, kasancewar basu bada mahimman bayyanai game da wanda ake zargi ko laifin da aka aikata ba, kana, sun nuna cewa har in adalci gwamnati take so tayi, sai ta hannunta wannan batu ga kotun kasar.

Wasu daga cikin al’umma sun dauka tamkar, gwamnati wasa da hankalin al’umma take yi, domin ya zama tamkar kamar rarashin mutane da suka aikata laifin gwamnati ke yi maimakon gurfanar da su a kotu. Musammamn ma idan aka yi la’akari da irin laifin da aka aikata na yiwa kasa zagon kasa wajen sayo makamai marasa inganci alhalin gwamnati ta samar da wadatattun kudade da za a sayo kayakin yaki.

A saurari rohoto cikin sauti daga Yusuf Abdoulaye a Yamai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG