Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Amurka Ta Tallafawa Sojojin Ruwan Nijar da Kayan Aiki


Sojojin Ruwan Nijar da Amurka ta basu horo ta kuma basu kayan aiki
Sojojin Ruwan Nijar da Amurka ta basu horo ta kuma basu kayan aiki

Bayan jami'an tsaron ruwan teku na kasar Nijar sun sami horo daga sojojin ruwan Amurka ne suka samu tallafin kayan aiki domin yakar masu fashi da makami akan ruwa da kuma safarar miyagun kwayoyi da 'yan ta'adda dake fakewa da tekunan suna kai hare-hare.

Ofishin jakadanci Amurka na kasar Nijar ne ya damkawa hukumomin kasar talllafin kayayyakin da za'a yi anfani dasu domin yin sintiri akan kogin Isa da na Kwara inda 'yan ta'ada da masu safarar kwayoyi ke ratsawa.

Wasu Jandarmomin Nijar da sojojin Amurka da suka basu horo
Wasu Jandarmomin Nijar da sojojin Amurka da suka basu horo

Kwamandan Muhamman Nasiru wanda yake shugabancin jami'an tsaro kan ruwa a yankin Yamai yace horan ya dauki sati biyu. An koya ma sojojin anfani da jiragen ruwa da yadda ake gyaran jiragen.

Shi kogin Isa ya hada Nijar da Mali da Najeriya yankin dake fama da yaki da ta'addanci. Saboda haka horon zai taimaka wurin yaki fa ta'addanci a kan ruwa.

Tallafin wani bangare ne na zunzurutun kudaden da Amurka ke kashewa kasar Nijar a fannin yaki da ta'addanci kamar yadda Alhaji Idi Barau, jami'in hulda da jama'a a ofishin jakadancin Amurka a Nijar ya bayyana..

Wasu cikin kayan aikin da aka ba jandarmomin Nijar
Wasu cikin kayan aikin da aka ba jandarmomin Nijar

Alhaji Barau ya fayyace kudaden tallafin. Yana mai cewa kayayyakin da Amurka ta baiwa Nijar sun kai dalar Amurka dubu dari biyar. A shekarar 2016 Amurka ma ta kashe dalar Amurkan miliyan goma sha shida domin tallafawa hukumomin Nijar a yaki da ta'addanci.

Kwamandan rundunar tsaro a yankin na Yamai ya yabawa wannan yunkurin na Amurka tare da cewa tallafin zai yi tasiri sosai wajen cin nasarar ayyukan da aka sa gaba.

Ga karin bayani daga rahoton Souley Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG