Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Amurka Ta Yi Tayin Taimakawa Gwamnatin Kasar Turkiyya


Shugaban Amurka Barack Obama ya yi tayin taimaka ma Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan, a binciken yinkurin juyin mulkin da aka yi masa a makon da ya gabata.

Fadar Shugaban Amurka ta White House ta ce Obama da Erdogan sun zanta ta waya jiya Talata, wato kwanaki hudu bayan yinkurin juyin mulkin da aka yi a Ankara. Obama ya fito fili ya ce Amurka za ta samar da taimakon da ya dace a binciken da ake yi.

Mutanen biyu sun kuma tattauna kan bukatar Turkiyya ta tasa keyar malamin addinin Musuluncin nan mai suna Fethullah Gulen da ke nan Amurka ya fuskanci tuhumar da ake masa na taka rawa a yinkurin juyin mulkin. Mai magana da yawun Fadar ta White House bai yi cikakken bayani ba kan matsayin Amurka game da yiwuwar tasa keyar Malamin, illa kawai cewa da ya yi, za a yanke shawarar ce kamar yadda yarjajjeniyar Turkiyya da Amurka ta tanada.

A tattaunawarsa ta waya da Erdogan, Obama ya yi matukar Allah wadai da yinkurin juyin mulkin, amma ya yi kiran da a gudanar da duk wani bincike da ladabtarwa game da yinkurin juyin mulkin ta yadda jama'a za su yi amanna da madafun dimokaradiyya da doka da oda, a cewar Fadar ta White House.

Tun farko a jiya Talatar, Turkiyya ta zafafa tankade da rairayar da ta ke yi tsakanin malamai da ma'aikatan gwamnati da ake zargi sun taka rawa a yinkurin juyin mulkin. Gwamnati ta kori mutane sama da 26,000 a yayin da ta kuma aika ma Amurka hujjojinta na cewa Gulen, wanda tsohon aminin Shugaba Erdogan ne, wanda a yanzu ke zama a jahar Pennsylvania ta Amurka, na da hannu a yinkurin juyin mulkin.

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG