Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Ekiti Za Ta Kawo Karshen Rikicin Makiyaya Da Manoma


Wasu shanun makiyaya

An ce idan ka ga gemun dan'uwanka ya kama da wuta , to ka shafa ma na ka ruwa, don haka gwamnatin jahar Ekiti, ganin yadda ake ta samun tashe-tashen hankula tsakanin makiyaya da manoma a sassan Najeriya, ta kuduri aniyar sasanta tsakanin makiyaya da manoma a jahar.

Yayin da tashe-tashen hankula tsakanin makiyaya da manoma ke dada ta’azzara a sassan Najeriya, inda ake ta asarar rayuka da dukiyoyi, gwamnatin Ekiti ta kudu maso yammacin Najeriya ta sha alwashin sasanta tsakanin manoma da makiyaya. Gwamnatin ta jahar Ekiti ta ce sam ba za ta lamunta da salwatar amfanin gona ko dabbobi ba.

A jawabinsa wajen wata addu’ar murnar cin zabe a watan da ya gabata, Mataimakin gwamnan jahar ta Ekiti, Otumba Bisi Ogbeyemi, ya ce, “Ban yadda wani mutum ya lalata amfanin gona ba; ai ni ma manomi ne. Haka kuma ban yadda wani manomi ya karkashe dabbobin makiyaya ba.” Ya ce sam babu abin da ya fi zaman lafiya dadi.

A nasa kira kan batun na zaman lafiya, babban limamin Majami’ar Cathedral Church of Emmanuel da ke birnin Addo Ekiti, Right Reverend Christopher Omotunde, ya yi kira ga shugabannin da su nuna imani da adalci a yayin da su ke aiwatar da duk wani abin da ya shafi jama’a.

Ga wakilinmu a Ibadan, Hassan Umaru Tambuwal da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG