Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Eritrea Ta Kwashe Shekaru 20 Ta Na Cin Zarafin 'Yan kasar


'Yan Eritrea dake kokarin arcewa daga kasarsu

Hukumar binciken da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa kan Eritrea tace shugaban kasa da jami'ansa sun dade suna cin zarafin 'yan kasar inda suke cin karensu ba babbaka

Wata Hukumar Bincike ta Majalisar Dinkin Duniya ko M-D-D da aka kafa don ta binciki zargin taka hakkokin bil adama da akace anyi a kasar Eritrea tace tana son a kafa wani Kwamitin musamman ko Kotu da zasu saurari irin zarge-zargen da ake yi wa shugabannin Eritrea din, wadanda akace sun fi shekaru ashirin suna taka hakkokin mutanensu yadda suka ga dama.

A cikin rahoton da Hukumar mai wakilai ukku ta bayar,kamar yadda daya daga cikin wakilan, Sheila Keetharuth ta gabatar, an nuna cewa abubuwan da ake zargin shugabannin na Eritrea da aikatawa sun hada da salwantar da mutane, ganawa wasu azaba da kuma kashe-kashen gilla na ganganci a hannun hukuma.

Hukumar Binciken ta MDD dai ta tara bayanan shaida daga wajen ‘yan kasar ta Eritrea su 833 a kasashe 13, ta kuma karbi rubutattun bayanai kamar 160.

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG