Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Ghana Da USAID Sun Samar Da Hanyar Koyar Da Yara Karatu Ta Radiyo


Radiyo
Radiyo

Lokacin da aka rufe makarantu a kasar Ghana a tsakiyar watan Maris saboda cutar coronavirus, nan da nan aka koma koyarwa ta yanar gizo da kuma talabijin.

Gwamnatin kasar Ghana tare da hadin gwiwar hukumar raya kasashe masu tasowa ta Amurka USAID, sun samarwa kananan yara shirye-shiryen radiyo dake koyawar miliyoyin dalibai.

Ana gabatar da shirin na tsawon sa’a guda kwanaki shida a cikin mako, kuma ana dogaro da koyarwa ne cikin wasa.

hukumar USAID ta na samar da shirye-shirye na koyar da karatu a Ghana, kafin ta hada hannu da gwamnati da wasu masu ruwa da tsaki wajen gabatar da shirin na radiyo.

Ministan Ilimin kasar Ghana, ya fadi cewa an tsara shirin ne don kananan yara kafin su fara firamare da kuma wadanda suke firamare kuma za a ci gaba har bayan annobar coronavirus.

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG