Gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun shi ya sanarda yarjejeniyar jiya Laraba a garin Abeokuta babban birnin jihar yayin da ya karbi ziyarar tawagar mutane takwas daga ma'aikatar aikin gona ta kasar Malaysia karkashin jagorancin Dotun Mohammed Hashim Abdullahi sakataren ma'aikatar. Gwamna Ibikunle Amosun ya cigaba da cewa ya kamata a sami kayan aiki na zamani da kayan noma na zamani da iraruwa ingantattu.
Kwamishanar Aikin Gona ta jihar Ogun Uwargida Ronke Shokefun ta ce wannan shi ne mataki na farko a yarjejeniyar da suka cimma. Ta ce sun ga ayyukan da suka yi a Malaysia kuma su ma suna soon su yi irin ayyukan. Shugaban tawagar daga Malaysia Dotun Mohammed Hashim Abdullahi ya ce sun kammala yarjejeniya tsakanin jihar Ogun da ma'aikatar gona ta Malaysia. Yarjejeniyar zata ta'allaka ne wurin bunkasa noman shinkafa da kwakwar manja da rogo da tumatur da tattasai da dai sauransu.
Hassan Umaru Tambuwal nada rahoto.