Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Kafa Hukumar Kula Da Jinyar Marasa Galihu


Ana duba yara a karamin asibiti dake kauyen Bagega a jihar Zamfara ta arewa maso yammacin Najeriya.
Ana duba yara a karamin asibiti dake kauyen Bagega a jihar Zamfara ta arewa maso yammacin Najeriya.

An kaddamar da Hukumar da zata rika daukar dawainiyar jinyar marasa galihu dake cikin al’umma a duk fadin jihar Bauchi.

An kaddamar da wannan shiri ne da ake kira BASHCMA a takaice a karamar hukumar Kirfi a matakin farko na aiwatar da shirin da za’a gudanar a dukan yankunan kananan hukumomi ashirin dake jihar

Shirin wanda aka kasa gida uku ya hada da bangaren da ya shafi kula da ma’aikata, da na wadanda basa aikin gwamnati, sai kuma na marasa galihu.

A hirar shi da Muryar Amurka, Shugaban hukumar a jihar Bauchi Dokta Mansur Dada, ya bayyana cewa, an kaddamar da ashirin ne ganin yadda duk da yake ana da kwararrun ma'aikatan jinya, da isassun magunguna da kuma asibitai, mutane da dama suna fuskantar matsalar kula da lafiyasu, sabili da rashin kudin biyan aikin jinya.

Bisa ga cewarshi, hukumar zata bada karfi wajen cike gibin da ake samu wajen kula da lafiya musamman abinda ya shafi talakawa masu karamin karfi wadanda da dama su ke mutuwa da cututukan da za su iya warkewa da sun sami jinya.

A jawabinsa, shugaban karamar hukumar Kirfi, Alhaji Garba Musa Bara, ya bayyana bada goyon bayan karamar hukumar don cimma burin Shirin.

Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Mohammed cikin sauti:

Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Kafa Hukumar Kula Da Jinyar Marasa Galihu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

XS
SM
MD
LG