Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Borno Ta Ce Gwamnatin Jonathan Ba Ta Taimaka Ma Ta Ba


Wasu 'Yan Gudun Hijira a Borno

Yayin da Hukumar Kwastam ta Kasa ke mika ma gwamnatin jahar Borno kayan tallafa ma 'yan gudun hijira a jihar, Gwamnatin ta Borno ta ce gwamnatin Jonathan ba ta yi wata rawar gani wajen tallafa ma ta ba

Mataimakin gwamnan jihar Borno Alhaji Zannan Umar Mustapha y ace gwamnatin da ta shude ba ta mata adalci ba game da matsalar Boko Haram da ta shafe shekaru sama da hudu ta na fama da ita. Da yak e karbar kayan tallafi daga wurin hukumar hana fasakwabri ta ‘CUSTOM,’ Alhaji Mustapha y ace a maimakon a dau matakan da su ka dace kan Boko Haram sai kawai aka maida al’amarin wata harkar siyasa; kuma duka-duka abin da gwamnatin taryyar Najeriya ta bas u shi ne Naira miliyan 200.

Y ace kananan hukumomi 22 na jihar Borno sun fada hannun Boko Haram lokacin da aka bas u naira miliyan 200 kawai; amma da kananan hukumomin jihar Adamawa biyar zuwa shida su ka fada hannun Boko Haram, sai aka ba ta naira biliyan hudu. Y ace babu irin wahalar da bas u sha ba a jihar Borno; hasalima, kusan dukkannin kananan hukumomin sun gudu sun tare a birnin Maiduguri, inda a yanzu haka ake da sansanonin ‘yan gudun hijira har 22. Y ace kusan watanni 6 kenan da rufe makarantu a jihar ta Borno kuma ana amfani da su a matsayin sansanonin ‘yan gudun hijira.

Mataimakin gwamnan, wanda ya jinjina ma hukumar ta kwastam, y ace jihar Borno ta kashe naira biliyan 11 wajen kula da ‘yan gudun hijirar. Shi kuwa Alhaji Tahir Musa Mataimakin Kwantarola-Janar na kasa kuma wanda ya wakilci Alhaji Abdullahi Dikko Inde Shugaban hukumar Kwastam na kasa, y ace ba daga asusun gwamnati aka tara gudunmowar ba, kuma ba daga irin kayakin da su kan kama ba ne, karo-karo ma’aikatar hukumar ta kwastam su ka yi bisa umurnin Shugaban hukumar na kasa.

Alhaji Musa y ace cikin abubuwa wajen 70 da su ka kawo akwai shinkafa da madara da indomi da tukwanen dahuwa da tufafi da takalma da tabarmu da dai sauransu. Y ace a baya ma sun ba da shinkafa wajen buhu 100,000, wato tireloli sama da 200.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG