Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Filato Tayi Taron Masu Ruwa da Tsaki Akan Samarda Burtali


Farfasa Sonni Tyoden, mataimakin gwamnan jihar Filato wanda ya kasance a taron

Gwamnatin jihar Filato tace bata yanke shawara akan samarda burtali ba, har sai ta tattauna da al'ummar jihar dalilin da ya sa ta shirya taron ke nan domin ta ji bahasin jama'a a kan lamarin

An yi taron tattaunawa ne da shugabannin al'umma da na matasa da shugabannin kananan hukumomi da jami'an tsaro da kungiyar dake fafutikar samarda zaman lafiya, wato "Search for Common Ground" ta shirya.

Mataimakin gwamnan jihar Filato Farfasa Sonni Tyoden ya shaidawa Muryar Amurka cewa gwamnatinsu zata yi anfani ne da shawarar da jama'ar jihar suka yanke game da batun kebe wuraren kiwo a jihar.

Farfasa Tyoden yace yanzu suna wayarwa mutane kawuna ne saboda gwamnati ta fada masu abun da take son yi su kuma su fadi nasu ra'ayin. Idan sun amince da matsayin gwamnati su bayyana. Idan kuma basu amince da matsayin gwamnati ba su fada.

Wasu da suka kasance wurin taron
Wasu da suka kasance wurin taron

Yace makon da ya gabata gwamnati ta zauna da sarakunan gargajiya da shugabannin matasa kana shi taron na yanzu tamkar ya hada kowa da kowa ne. Idan sun yadda a kebe wasu filaye to magana ta kare. Idan basu yadda ba sai su fadi abun da za'a yi.

Shugaban kwalajin horas da dalibai kan kula da dabbobi Farfasa Garba Sharubutu yace batun kebe wuraren kiwo abu ne da ya dace. Yace abu ne wanda yakamata da an fara shi tuntuni saboda yawan yawon kiwo ba zai haifar da da mai ido ba. Yace dabbobin da ake yawo dasu basa bada nama ko nono sosai. Amma idan an kebesu wuri guda ana ciyar dasu za'a samu nama da nono sosai.

Dangane da cewa wasu zasu ga kamar an kwace filaye ne an ba Fulani sai Farfasa Sharubutu yace wannan jahilci ne. Mutane sun dauka kamar an barwa Fulani kadai kiwon shanu ko dabbobi ne. Yace babu zancen ba Fulani filayen mutane kuma a yanzu ba Fulani kadai ba ne suke kiwon shanu.

Shugaban karamar hukumar Jos ta Gabas Dr. Samuel Ibrahim Pate yace kebe wuraren kiwo zai taimakawa al'umma matuka, kuma zai kara dangantaka tsakanin manoma da makiyaya.

Shi ma shugaban kungiyar "Search for Common Ground" wadda ta shirya taron Mr. Shemil Idris yace sun shirya taron ne domin hada kan masu ruwa da tsaki su tattauna su fahimci juna domin hana aukuwar tashin hankali.

Turawa Amurkawa na kungiyar "Search for Common Ground" da ta shirya taron
Turawa Amurkawa na kungiyar "Search for Common Ground" da ta shirya taron

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

XS
SM
MD
LG